Akaro na biyu Tiktok sun kara sawon bidiyo daga minti uku zuwa minti goma


 


Shahararren shafin sada zumunta dake tashe yanzu Tiktok sun fidda sabon tsarin da zai bawa masu saka bidiyo a shafin su daman daura bidiyo har na minti goma,kwanakin baya tiktok sun kara tsawon video da za’a iya daurawa daga minti minti daya zuwa minti uku yanzu kuma sun mayar minti goma.

A yanzu dai Tiktok ya zama babban kalubale ga kamfanin Youtube,sai dai wasu na ganin babu abunda wannan chanji da tiktok din suke kawowa zaiyi wa Youtube domin youtube sun riga da sunyi nisa ta bangaren fasahar bidiyo da kuma biyan masu kirkirar bidiyo.

Suma masu amfani da manhajan Tiktok wasu na ganin wannan sabon tsarin a matsayin wani karin aki sakamakon ba kowaye bane zai iya tsayawa yayi bidiyo har na tsawon minti goma,wasu kuma na ganin hakan a matsayin babban daman da zai basu daman yin sabbin bidiyo masu tsayi.

Wanna tsarin yana zuwa ne bayan kamfanin meta Facebook sun kaddamar da tsari mai kama da tiktok a cikin manhajan facebook wanda suka kira da suna Reels,inda zaka iya daura bidiyo na tsawon minti daya, yanzu dai da alama facebook ne zai koma tiktok inda tiktok kuma ya kama hanyar tinkarar Youtube.

Post a Comment

Previous Post Next Post