Kamfanin MTN sun sayi Filaye 144 a Duniyar yanar gizo (metaverse)

 




Metaverse wani duniya ne na musamman amfa a yanar gizo ba a zahiri ba, inda ake iya malakar fili har ma ayi gini kaman dai yanda muke rayuwa a wannan duniyar ta zahiri haka shima rayuwar metaverse yake bambamcin kawai shine metaverse dai duniya ce amma a cikin yanar gizo iya abunda zamu iya fada kenan yanzu akan metaverse.

Tuni aka fara sayar da filaye a metaverse inda mutane da dama da kuma kamfanoni na fasaha dama wanda bana fasaha ba suke ta ribibin sayan fili a duniyar na yanar gizo,kamfanin MTN ya shiga sahun kamfanoni wajen mallakar filaye a metaverse inda suka sai filaye har guda 144 daga hannun daya daga cikin dillalan metaverse wanda ake kiran su da Ubuntuland.

Ubuntuland dillalai ne a duniyar yanar gizo wanda kamfanin Africarare and Mann Made Media suka samar domin baje kolin al’adu da kuma sauran abubwan da suka shafi Afrika kama daga fasaha wasanni da sauransu a duniyar na yanar gizo.A wurin su ne MTN suka sayi katafaren filaye a duniyar yanar gizon.

A yanzu haka dai MTN sune kamfani na farko a Afrika da suka fara sayan fili a duniyar yanar gizo ma’ana metaverse,koh me MTN zasu fara ginawa a filayen da suka sayan kuma yaushe zasu fara yin gini wannan amsan duk kamfanin MTN ne zasu iya bayarwa.

Techausa muma zamu fara kokarin tara kudin da zamu sayi fili na musamman a duniyar yanar gizo.


Post a Comment

Previous Post Next Post