SAMSUNG GALAXY S23 ULTRA: Waya na musamman daga company samsung.

Samsung Galaxy S23 Ultra waya ce mai kyau dakuma inganci daga kamfanin Samsung, tana dauke da fasaha masu yawa wanda tana daya daga cikin manyan wayoyi. Ga wasu muhimman bayanai game da wannan wayan:

Screen:

Yana da screen mai girman inci 6.8 na Dynamic AMOLED 2X tare da 1440 x 3088 pixels, yana ba da hoto mai haske da launuka masu kyau.

Screen in wannan wayan yana da refresh rate 120Hz.


Camera:

Abaya yana dauke da babban Camera mai girman 200MP, wanda ke ba da damar É—aukar hotuna masu kyau.

Har ila yau, yana da Camera mai girman 12MP, da kuma camera wanda in kayi zooming Mai girman 10MP.

Kamara ta gaba tana da 12MP.

Yana dauke da chipset na Snapdragon® 8 Gen 2 Mobile Platform for Galaxy, wanda ke ba da ingantaccen aiki.

Yana zuwa da  RAM na 8GB ko 12GB, da storage 256GB, 512GB, ko 1TB.

Girman Pixel na  Bidiyo

8K@30fps (7680 × 4320 pixels)

4K@60fps, 30fps (3840 × 2160 pixels)

1080p@240fps, 60fps, 30fps (1920 × 1080 pixels)

720p@960fps (1280 × 720 pixels) – Super Slow Motion

Qarin bayanai gameda video da wannan wayan take dauka:

Super HDR: Yana ƙara haske da launuka don ingantaccen bidiyo.

Optical Image Stabilization (OIS) & Electronic Image Stabilization (EIS): Don rage girgiza yayin daukar Video.

Super Slow Motion Mai girman 960fps.

Tana dauke da Auto Focus Tracking wanda yayinda kake daukar video zata ringa bibiyar fuskar ka.


Galaxy S23 Ultra na ba da damar recording a 8K@30fps.

Yana da baturi mai ƙarfin 5000mAh, wanda zai iya ɗaukar rana ɗaya ko fiye kana amfani dashi.

Yana chaji a 45W, wanda ke ba da damar caji cikin sauri.

Yana da speakers biyu don sautin sitiriyo.

Yana dauke da  S Pen, wanda ke ba da damar rubutu da zane kai tsaye akan Screen .

Yana da kariya daga ruwa da Æ™ura na  IP68.

Post a Comment

Previous Post Next Post