IPHONE 15 PRO MAX: Waya daga kamfanin Apple.

iPhone 15 Pro Max wayace ce mai inganci daga kamfanin Apple, tana da sabbin technology da ingantaccen tsarin daukar bidiyo. Ga wasu muhimman bayanai game da wannan wayan:

Screen:

Yana da screen mai girman inci 6.7 na OLED (Super Retina XDR) tare da 2796 x 1290 pixels, yana ba da hoto mai haske da launuka masu kyau.


Camera:

Babban Kamara na wannan wayan yana da girman 48MP tare da fasahar (Quad-Pixel), wanda ke ba da damar É—aukar hotuna masu kyau da cikakken quality.

Daukar Bidiyo: Yana recording na video har zuwa 4K a 60fps tare da HDR da Dolby Vision.

Sannan wannan wayan yanada Cinematic Mode: Yana ba da damar rikodin bidiyo tare da  nuna komai da tsabta, daga gaba har baya.
(depth of field) don ƙirƙirar tasirin sinima.

Action Mode: Wannan wayan camera nata  yana ba da damar rikodin bidiyo mai sauri da motsi tare da rage girgiza, har zuwa 2.8K a 60fps.

ProRes Recording: Don masu sana'a, yana ba da damar rikodin bidiyo a tsarin ProRes har zuwa 4K a 60fps.

Slo-Mo: Yana goyan bayan rikodin bidiyo mai jinkiri (slow-motion) a 1080p har zuwa 240fps.

Spatial Video Capture: yana ba da damar rikodin bidiyo tare da tasirin sarari, wanda za a iya kallonsa a kan na'urar Apple Vision Pro.

Bayani gameda chipset da Storage na wannan wayan:

Yana amfani da tsarin  A17 Bionic, wanda ke ba da ingantaccen aiki da saurin sarrafawa.

Storage na wannan wayan akwai mai 256GB, 512GB, da 1TB.

Hakanan agefen ƙiraye ƙiraye na waya: An yi shi da kayan titanium, wanda ke ba da ƙarfi da sauƙin nauyi ta yanda kana tura koda ƙirane a take zai tafi.

Wannan wayan yana dauke da Face ID domin unlock na wayan dakuma bada tsaro ga wasu Application da za a iya sa musu Password duk za a iya sai tasu da wannan Face ID.

A ɓangaren battery apple basu Bayyana girman battery da wannan wayan yake zuwa dashi ba sai dai ga wasu bayanai gameda wannan battery.

Kallon bidiyo: Har zuwa awanni 20

Kallon bidiyo (ta hanyar yanar gizo): Har zuwa awanni 16

Sauraron sauti: Har zuwa awanni 80.

Sannan wannan wayan yana support na 2G, 3G, 4G LTE, da 5G NR.

Post a Comment

Previous Post Next Post