Menene refresh rate? A sauƙaƙe, yana nufin sau nawa allo(sikirin) ke sabuntawa refireshi kanshi a kowace daƙiƙa don nuna sabbin hotuna. Ana auna shi da Hertz (Hz). Allo (sikirin) mai 60Hz yana sabuntawa sau 60 a kowace daƙiƙa, yayin da allo (sikirin) mai 120Hz ke sabuntawa sau 120 a kowace daƙiƙa.
Misalai Ta Gaske
Misali kana duba shafukan sada zumunta a kan allo (sikirin) mai 60Hz—yana da kyau, amma zai iya É—an yi kamar yana tsalle-tsalle. Sai ka gwada hakan akan allo mai 120Hz sai ka ga duk motsi suna jin kamar santsi sosai. Wannan shi ne abin mamakin refresh rate mai girma!
Wani misali kuma shi ne wasanni(games). Akan (sikirin) allo mai 60Hz, wasanni masu saurin kamar PUBG ko Call of Duty Mobile suna iya yin É—an jinkiri a lokutan zafi. Amma da allo (sikirin) mai 120Hz, motsin ka da kuma hotuna suna dacewa sosai, suna ba ka fa'idar gas.
Ina Refresh Rate Mai Girma Ke Bambanta?
Refresh rate mai girma tana nuna bambanci a wurare da dama:
Duba shafuka kamar Instagram ko Twitter? Motsin yana daÉ—i sosai.
Kallon bidiyoyi masu kyau ko motsi? Komai yana bayyana kamar gaske.
Wasanni (games).? Zaka ji kamar kana ciki sosai tare da saurin amsawa da tsabta.
Shin Akwai Matsaloli?
Eh, refresh rate mai girma abin burgewa ne, amma yana cin Æ™arfin batir sosai. Duk da haka, na’urori da dama suna bayar da adaptive refresh rate, inda ake canzawa tsakanin 60Hz da 120Hz gwargwadon abin da kake yi, domin a sami daidaito tsakanin aiki da tsawon lokacin batir.
Kammalawa
A takaice, refresh rate mai girma yana inganta yadda muke hulÉ—a da na’urorin mu. Idan kana siyan sabon waya, ka yi la’akari da wacce ke da 90Hz ko 120Hz display—zai sauya rayuwa wajen aiki da nishaÉ—i."
"Wannan kenan a yau! Idan ka ga wannan ya amfanar, kada ka manta ka yi like, share, da subscribe don karin bayani game da fasaha. Sai mun haÉ—u a gaba!
adamisahmuhammad210@gmail.com
ReplyDeleteLabaran issaka
ReplyDeletePost a Comment