Menene Computer
Kwamfuta na’ura ce mai aiki da kwakwalwa, wajen karba da sarrafawa da adanawa da kuma mika bayanai, a sigogi daban-daban.
kwamfuta na tattare ne da manyan bangarori guda biyu;
1.bangaren gangan jiki, wanda aka fi sani da Hardware,
2.Bangaren (manhaja),Wadda aka fi sani da Software a turance.
Menene Hardware?
Hardware ya shafi duk wani bangare na kwamfuta wadda zaka iya gani kokuma ka taba. Misali mouse, monitor da sauransu.
Menene Software?
Software ya shafi bangare kwamfuta Wanda yake da alhakin gudanar wa da kuma samar da sadar sakanin mai aiki da computer da kuma ita kwamfuta. Misali Microsoft Word, Google Chrome. Da sauransu.
Post a Comment