HAUWEI MATE 50 PRO

Huawei Mate 50 Pro wata wayar salula ce ta zamani da kamfanin Huawei ya ƙaddamar a shekarar 2022. An tsara ta don ba da ingantaccen aiki da fasali na musamman ga masu amfani.

Bayani game da wannan wayan:

Screen (Display): 6.74-inch OLED tare da ƙudurin 2616 x 1212 pixels, yana ba da hoto mai haske da launuka masu kyau.

Tsarin Aiki na (Processor): Qualcomm Snapdragon 8+ Gen 1 4G, wanda ke ba da ingantaccen aiki da sauri.

Memory (Storage): 8GB na RAM tare da 256GB ko 512GB na memory, kuma ana iya faÉ—aÉ—a ajiyar ta hanyar katin NM (Nano Memory) har zuwa 256GB.

Kyamarori (Cameras):

Baya (Rear): Babban kyamara mai girman 50MP tare da fasahar Ultra Aperture, 13MP ultra-wide angle, da 64MP telephoto kyamara mai goyon bayan 3.5x optical zoom da 100x digital zoom.

Gaba (Front): Kyamara mai girman 13MP don hotunan kai masu kyau.

Baturi (Battery): 4700mAh tare da goyon bayan caji mai sauri na 66W, caji mara igiya na 50W, da kuma caji na baya (reverse wireless charging).

Tsarin Aiki na (Operating System): HarmonyOS 3.0 ko EMUI 13, bisa ga yankin da aka sayi wayan.


Kariyar Ruwa da Kura: na IP68, yana nufin na'urar tana da kariya daga ruwa da kura.

Kariyar screen: An ƙarfafa screen in da fasahar Kunlun Glass, wanda ke ƙara ƙarfin jurewa faɗuwa da rauni.

Farashin Huawei Mate 50 Pro ya bambanta bisa ga wuri da dillali. A wasu kasuwanni, farashin ya kasance kusan $649.99 wacce take zuwa da 256GB ROM da 8GB RAM.

Huawei Mate 50 Pro na ba da haÉ—in fasali masu Æ™arfi da Æ™ira mai kyau, tare da kyamarori masu inganci da fasahar caji mai sauri. Wannan ya sa ta zama zaÉ“i mai kyau ga masu neman wayar zamani mai inganci da fasali na zamani. 

Post a Comment

Previous Post Next Post