Redmi Note 14 5G: Sabuwar Waya Mai Cike da Inganci


Redmi Note 14 5G ya kasance waya me cike da ƙarfi da salo don ba wa masu amfani da ita duk abunda suke Neman ta musamman. Ga bayani dalla-dalla kan wannan wayar:


Tsari Da sikirin

Wayar tana da allo mai girman 6.67-inch AMOLED tare da FHD+ da rifireshi mai Gorman 120Hz na sabunta hotuna. Har ila yau, tana da haske mai ƙarfin 2100 nits, wanda ke tabbatar da gani mai kyau koda a rana ko cikin dare.

Ƙarfin Aiki

Wannan waya tana amfani da MediaTek Dimensity 7025 processor tare da RAM har zuwa 12GB da fon memory  har 512GB, wanda za a iya Æ™ara shi zuwa 1TB ta hanyar microSD. Wannan fasaha tana da saurin aiki ga ayyuka daban-daban.
Kyamarori

Redmi Note 14 5G tana dauke da tsarin kyamarori guda uku a baya, ciki har da babban kyamara mai girman 108MP wadda ke ɗaukar hotuna masu ƙyau. Kyamara ta gaba kuma tana da megapixels 20 don selfies masu kyau.

Batir da Caji

Tana da batir mai É—aukar lokaci mai tsawo na 5110mAh wanda za a iya cajewa da sauri a  45W fast charging.

Sauran Fasalin Wayar 

Wayar tana da lasifikan Dolby Atmos® don sauti mai kyau, kariyar ruwa IP64, da tsarin Xiaomi HyperOS wanda ke bada sauÆ™i wajen amfani.

Redmi Note 14 5G ta dace ga masu sha’awar fasaha da kayan aiki masu inganci a farashi mai sauÆ™i.


Post a Comment

Previous Post Next Post