iPhone 15: Shin Har Yanzu Zaka iya Saya a Shekarar 2025 Bayan Fitowar iPhone 16?

Jerin iPhone 15, wanda aka gabatar a watan Satumba 2023, ya zama babban ci gaba a cikin layin wayoyin Apple, yana ba da kyakkyawan gasali, an haɓaka kayan aiki, da sababbin fasalulluka waɗanda suka dace da bukatun masu amfani daban-daban.


Tsari da allan Wayar 

iPhone 15 da 15 Plus sun É—auki fasalin Dynamic Island, wanda a da yake na musamman ga Pro da Pro Max kawai a daa, suna maye gurbin tsohon notch kuma suna ba da fasali me kew akan allan gabar Wayar.  Dukkanin samfuran sun Æ™unshi allan Super Retina XDR OLED tare da Æ™arin haske da ya kai har nits 2,000  don amfani a waje, har ma a karkashin hasken rana, wanda ya tabbatar da bayyanan hasken allan  sosai.


Kayan Aiki da Ayyuka

jerin iPhone 15 na sanye  da A16 Bionic chip, wanda ke ba da Æ™arfin da ya dace da ayyukan multitasking da aikace-aikacen da ke buÆ™atar Æ™arfi. Babban canji shi ne canza daga tsohuwar Lightning connector zuwa USB-C ports, wanda ya dace da matsayin sauranmasana'antu kuma ya sauÆ™aÆ™a caji da musayar bayanai. Duk da haka, yana da mahimmanci a lura cewa iPhone 15 da 15 Plus suna dauke da USB 2.0, yayin da samfurin Pro na dauke da  USB 3.2 Gen 2.


Tsarin Kyamara

An samu babban ci gaba a tsarin kyamara, tare da kamara Mai  48MP wanda zai iya samar da hotuna masu inganci na 24MP, babban cigaba  idan aka kwatanta da tsofaffin hotunan 12MP. Wannan ci gaban ya ba da damar samun hotuna masu kyau da cike da launi, suna dacewa da masu daukar hoto na yau da kullum da na Æ™wararru.


Rike Baturi fa?

Rayuwar batir ta inganta sosai, tare da iPhone 15 mai dauke da baturi 3,349mAh idan aka kwatanta da iPhone 14 mai 3,279mAh. Wannan haɓaka ya baiwa masu amfani damar amfani da wayar na dogon lokaci, yana goyon bayan ayyukan na'urar tsawon yini.


Shin an karbe su a kasuwa ?

Bayan fitowa, jerin iPhone 15 sun samu karÉ“uwa sosai saboda sabunta fasalullukansa, gami da Dynamic Island, Æ™arin Æ™arfin kyamara, da kuma canjin zuwa haÉ—in USB-C. WaÉ—annan canje-canje sun kasance a matsayin ci gaba wajen sauÆ™aÆ™a wa masu amfani da inganta aikin na'ura. Duk da haka, wasu masu amfani sun lura cewa wadannan cigaban, duk da cewa suna da muhimmanci, sun fi karkata zuwa ga cigaba a hankali maimakon canji mai girma, wanda hakan ya sanya wasu ke yin la’akari da ko cancanta su canza nan take idan suna da sabbin samfura

Daga Karshe 

Jerin iPhone 15 ya wakilci ci gaba mai ma’ana a cikin zane da fasahar Apple, yana bayar da fasali da ke kara jin daÉ—in amfani da daidaita da ka’idojin zamani. Ga masu amfani da tsoffin samfuran iPhone, iPhone 15 ya ba da dalili mai karfi na yin sabuntawa, yayin da wadanda ke da sabbin na’urori za su iya yin la’akari da ribar idan aka kwatanta da irin ci gaban da aka samu.

Post a Comment

Previous Post Next Post